Surah 104 · 9 verses · Abubakar Mahmood Jummi

Surah Al-Humazah in Hausa

In English with tafsir

بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

104:1

وَيۡلٌ لِّكُلِّ هُمَزَةٍ لُّمَزَةٍ

Bone ya tabbata ga duk mai nune, mai zunɗe (mai raɗa)

104:2

ٱلَّذِي جَمَعَ مَالًا وَعَدَّدَهُۥ

Wanda ya tara dũkiya, kuma ya mayar da ita abar tattalinsa

104:3

يَحۡسَبُ أَنَّ مَالَهُۥٓ أَخۡلَدَهُۥ

Yana zaton cẽwa dũkiyarsa za ta dawwamar da shi

104:4

كـَلَّاۖ لَيُنۢبَذَنَّ فِي ٱلۡحُطَمَةِ

A'aha! Lalle ne zã a jẽfa shi a cikin Huɗama

104:5

وَمَآ أَدۡرَىٰكَ مَا ٱلۡحُطَمَةُ

Kuma me ya sanar da kai abin da ake ce wa Huɗama

104:6

نَارُ ٱللَّهِ ٱلۡمُوقَدَةُ

Wutar Allah ce wadda ake hurawa

104:7

ٱلَّتِي تَطَّلِعُ عَلَى ٱلۡأَفۡـِٔدَةِ

Wadda take lẽƙãwa a kan zukata

104:8

إِنَّهَا عَلَيۡهِم مُّؤۡصَدَةٌ

Lalle ne ita abar kullẽwa ce a kansu

104:9

فِي عَمَدٍ مُّمَدَّدَةِۭ

A cikin wasu ginshiƙai mĩƙaƙƙu

Translation: Abubakar Mahmood Jummi.